28 Nuwamba 2020 - 12:30
Iran: Rauhani Ya Zargi Masu Girman Kai Na Duniya Da Isra'ila Da Kashe Shahid Fakhri Zadeh

Shugaban kasar na Iran Dr. Hassan Rauhani ya fitar da bayani danage da kisan gillar da aka yi wa Shahid Fakhry Zadeh a jiya Juma’a da cewa;

ABNA24 : Babu shakka wannan aikin na ta’addanci yana nuni ne da gajiyawar magautan Iran wajen fuskantar ci gaban ilimin da ta samu, sannan kuma yana nuni bakar gabar da suke da ita.

Shugaban na kasar Iran ya ci gaba da cewa; Makiyan Iran su kwana da sanin cewa; Al’ummar Iran za ta mayar da martani, tare da jaddada cewa hanyar da shahid Fakhry Zadeh ya shata za ta ci gaba ba tare da tsayawa ba.

342/